An Sace Hakimi Tare Da Tawagarsa Da Kananan Yara A Jihar Bauch
Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa wasu 'yan bindiga da ba a san kosu waye ba, sun sace wani Hakimi hade da kananan yara a karamar hukumar Toro.
Bayanai na cewa an sace hakimin gundumar Tama, Malam Adamu Yakubu ne a gidansa, da kuma wasu kananan yara biyu a gidan makotan hakimin ranar Asabar da misalin karfe biyu na dare.
Sakataren hakimin yankin Lame, Adamu Muhammad, ya tabbatar wa Kafar Yada Labarai Ta BBC cewa 'yan bindigar sun yi kuma harbe-harbe a yankin kafin su yi awon gaba da mutanen zuwa wani wuri da har kawo yanzu ba a tabbatar da ko ina ne ba.
Ba a tabbatar da makasudin sace Hakimin da kuma talakawan nasa ba, amma bayanai na cewa 'yan bindigar sun bar lambar wayarsu da cewa a tuntube su, amma kawo yanzu babu tabbacin ko an samu magana da su.
A baya-bayan nan dai ana samun yawaitar sace-sacen mutane ana garkuwa da su domin karbar kudin fansa a jihar Bauchi da ma wasu jihohi na Arewaci da Kudancin Kasar Nan.
No comments:
Post a Comment