A baya mun kawo muku bayanai akan sirrin da ke tattare a cikin Kankana da kuma fa’idojin da ta ke da shi ga lafiyar mu.
Toh amma ko kun san cewa shan kankana tare da abinci ya na kashe amfanin ta?
Maimakon a samu amfanin, sai dai ma ta haifar da matsaloli kamar su kumburin ciki, yawan gyatsa da sauransu.
Lokacin da ya fi muhimmanci a sha kankana shi ne da sanyin safiya kafin a ci komai, sannan a bar ta ita kadai a ciki na tsahon akalla mintina 30.
Ko kuma da daddare a lokacin da abincin da aka ci na karshe ya gama narkewa a ciki.
Idan mutum zai jimiri yin hakan to tabbas zai ga banbanci, kama daga kan fatarsa zuwa karfi da lafiyar jikin shi.
Ga fa’idojin da ke tattare da shan kankana da sanyin safiya ko kuma kafin a ci komai:
1. Gyara fatar jiki da magance ta daga kamuwa da matsalolin da zafin rana ke haifar wa.
2. Rage yiwuwar kamuwa da cutar daji da hawan jini da sauran su.
3. Inganta samun barci mai kyau.
4. Inganta karfin jiki da akalla kaso 23 cikin dari.
5. Kara saurin warkewar ciwuka da matsalolin fata da ninki uku.
6. Kara lafiyar lafiyar ma’aurata wajen gudanar da ibadar aure.
Sinadarin Arginine da ke cikin kankana na kara karfin maza kamar yadda magunguna kamar su ‘Viagra’ ke yi.
7. Inganta garkuwar jiki saboda kankana ta na dauke da sinadarin da ke shiga cikin jini ya wanke kwayoyin cutar da ke ciki.
An fi samun alfanun kankana idan aka shanye ta gaba daya har bawon ta da kwallayen ta, saboda su ma suna dauke da nasu sinadaran masu dumbin alfanu.
No comments:
Post a Comment