A Najeriya, mahukunta na wani sabon yunkuri na kyautata safarar kayan gona zuwa kasashen waje da nufin fadada kafofin samun kudin-shiga mai makon dogaro da mai.
To sai dai kuma wasu 'yan kasuwa, sun ce duk wani kokari da za suyi don tallata kayan Najeriya zuwa kasashe ketare, da wuya ya yi tasiri.
'Yan kasuwar dai na cewa suna cin karo da matsaloli a wannan harka, ciki har da karancin jari da rashin darajar kayan Najeriyar a kasuwannin kasashen Turai.
Alhaji Kamal Abdulkadir Mustapha, dan majalisar 'yan kasuwar jihar Kano ne da ke arewacin Najeriya, wanda kuma ke fataucin kaya zuwa kasashen turai, ya shaida wa BBC cewa, kayansu na fuskantar kalubale sosai a kasashen waje, saboda yawanci 'yan Najeriya sun yi suna wajen aika abubuwa wanda suke jabu, marassa nagarta, hakan ya sa idan ka kai kaya daga Najeriya ake fuskantar kalubale.
Alhaji Kamal, ya ce " Wannan dalili ne ya sa wasu 'yan kasuwar Najeriyar kan gwammace su kai kayansu Nijar ko Ghana ko kuma Cotonou, domin su auna kayansu su tura su ta can, don su samu biyan bukata wato ta yadda idan an kai su kasashen waje za a saye su daraja".
A kan wadannan dalilai, 'yan kasuwar suka ce dole ne sai gwamnati ta taimaka wajen kare martabar kayayyakin da suke samarwa a idon kasashen duniya, idan ana so kasuwancinsu ya bunkasa.
To yanzu dai, gwamnatin Najeriyar ta ce bisa la'akari da irin kalubalen da 'yan kasuwar ke fuskanta, hakan ya sa hukumar bunkasa fataucin kayan Najeriya zuwa kasashen waje ta fito da wani shiri na kara wa 'yan kasuwar kwarin gwiwa.
Hukumar dai ta na hada wasu fatake a wasu manyan biranen kasar domin wayar musu da kai a kan sabon shirinta game da bunkasa fitar da kayayyakin amfani gona zuwa kasashen waje.
No comments:
Post a Comment