Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani jirgi mara matuki da aka kera a cikin gida, irinsa na farko a kasar.
Jirgin wanda cibiyar kere-kere ta dakarun sojin saman Nijeriya ta yi, zai yi amfani wajen yaki da 'yan ta-da-kayar-baya da kuma masu fashi da makami.
Akwai tanadin kera jirgin da yawan gaske, har ma da yiwuwar fitar da shi zuwa ketare.
Nijeriya na fama da barazanar tsaro rututu ciki har da ta 'yan ta-da-kayar-baya a arewa maso gabas,
Akwai kuma matsalar matasa masu gwagwarmaya da makamai a yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ga kuma rikicin makiyaya da manoma.
No comments:
Post a Comment