Saturday, 12 February 2022

Kalaman soyayya 2

2- Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.

3- MASOYI na, Kaine wanda ka dace da sarautar zuciya ta don haka na baka ita kyauta, Zan iya aiwatar da komai har idan ina jin kalaman ka masu sanyaya zuciya, Na yarda da kai na aminta da kai don haka na mallaka maka kaina.

4- Shiru na baya nufin na mantaki, ko bani ki kulawa, saboda ko yaushe a cikin zuciya ta Kece kullum kike kusa da ita, sai da saife.

5- Matata Uwar ‘ya’yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d’aya, ina cike da zumud’in son dawowa domin cin girkin ki mai dadi. ki kulamin da kan ki, sai na dawo. Ina son ki matata.

No comments:

Post a Comment