Saturday, 12 February 2022

kalaman soyayya 3

❤ ❤ 😍 💖 ❣ 💕 

1- Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa da juna. Amma ina son, ki san da cewa, a duk inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da tinaninki a matsayinki na mata ta da nake matu’kar so da ‘kauna ba. Ina nan tafe a hanya zuwa gare ki. Ki kasance mai tina cewa, ba ni da kamar ki. Ina Son Ki.
2- Masoyiya ta a duk lokacin da naji muryar ki nakan samu natsuwa a zuciya ta, Murmushin ki a gare ni yafi aban kyautar duniya, Fiskar ki a kullum haske take kara yi musamman idan kina murmushi, Idan kikai fushi sannan ne kike dada kara kyan gani.
3- A kullum bani da burin sauraren wani zance in ba naka ba masoyina.
4- SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani dan karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki.

No comments:

Post a Comment